Breaking

Tuesday, November 13, 2018

Kece Sila Page 1&2

♥♥💍♥♥  

     💍♥💍

         💍


    🌹💖🌹 *KECE SILA* 🌹💖🌹

         (other name= *CIKIN RAINA* )


                             ♥♥💍♥♥

                                 💍♥💍

                                     💍

   



Na= *AYSHA B/AESHAB*💌



🐄 *Real hausa fulani writer's forum*






*Abinda littafin ya kunsa amma a taqaice*


stars din littafin: *SAFIYYA* DA *AMEEN* (AL-AMEEN)... Safiyya yarinyace er gata saidai sanadiyyar wata qaddara wacce tasa aka kashe mahaifinta yasa aka koresu daga gidan da suke... Safiyya tasha gwagwarmayar rayuwa wanda bata saba ba, ta fuskanci wulaqanci wanda yasa annurin fuskarta daukewa burinta ya zamo ta dauki fansa ne kawai kan Ameen wanda a zatonta shine ya kashe mahaifinta ya kwace gidansu,,,,, ku biyoni kuji 

1. shin tana daukar fansar ta cika burinta?

2. shin Ameen ne ya kashe mahaifinta ya kwace gidansu da dukiyarsu?

3. to waye shi Ameen dinma kuma ya halayyarshi take?

4. wacce irin fansa takeson dauka kan Ameen?

5. me mahaifinta yayiwa Ameen?

6. Ta ina sunan littafin (KECE SILA) ya dace da labarin?

dama wasu tambayoyin duk amsar na cikin littafin.. ku kasance tareda ni Aysha b...



LITTATTAFAN MARUBUCIYAR;

*SUMAYYA*

*Y'AR UWATA*

*AKLAAQIN NAFS ('Dabi'un zuciya)*

*SOYAYYAR ASMAD*

*SO FARUWA YAKE* 

SAI KUMA KECE SILA




*sadaukarwa ga masoyana* 💌




               💍 *PAGE 001* 💍


                        


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


6 na yamma 


en mata ne guda biyu daya shekarunta 21 dayar kuma shekarunta 16 sannan yarinyar er qarama wacce bata wuce shekaru 7 ba, se wata dattijuwa zatai shekaru 56,,,


 yanayin da suke ciki kadai ya isa ya tabbatr maka sun galabaita er shekaru 16 wacce ta kasance cikin jinsin farare me zubin larabawa tana sanye ne da atampa riga da skirt sai dankwalin kanta daya dan zame wanda ya bayyanar da gashinta mai laushi kwantacce saidai ba baki ne ba ta yafa gyalenta,, 


hawaye sosai take suna tafe a bakin hanya yayinda motoci suke wucesu, kowannensu dauke da trolley


 yayinda er shekaru 21 take jan trolley biyu da jakar hannu, ita er shekaru 21 din duk kyawun qanwarta se naga ashe nafila ne dan kuwa ban san ta yadda zan fasalta muku kyawun ta ba dan fatarta har wani maiko take tana kyalli kallo daya zakayi musu kasan tafi qanwarta kyau, daga idanuwa, hanci, lips face dinta irin innocent face ne kalar shiru shiru da rashin hayaniya....


zubin jikinsu ba daya bane ita babbar bata da jiki sosai, qaramar farar tafi shape tafi cika dukda itama yayar tanada shape amma bata da cika kamar qanwar tata, ko kadan babu alamar wahala a fatarsu sedai fuskarsu ta nuna a kwanakin nan suna jigata


dattijuwar ta dubi qaramar wacce keta faman zubda hawaye tace

"dan Allah *SAFARA'U* ki dena kukan nan haka mana" 

fuska a murtuke dukda bakincikin dake ranta be hanata cewa

" *IYA* dan Allah ki dena bata min suna ni sunana *SAFRAH* " tana qare zancen nata ta cigaba da zubda hawayenta,


itadai iya batason wannan kukan, kallon babbar tayi wacce babu ko digon annuri a fuskarta kana dubanta zaka san kukan zuci kawai takeyi, tareda zallar bakinciki a tattare da ita wanda ya bayyana a kyakkyawar fuskarta, 


" *SAFIYYA* dan Allah kiyiwa SAFRAH magana ta dena zubda hawayen nan haka nan"

Safiyya batace komai ba, yarinyar er qaramar ce ta dubi iya tace

"iya ni yunwa nakeji kuma inajin bacci" 

sai lokacin safiyya tayi magana cikin muryarta mai dadin sauraro, wacce take da sanyi sosai, dan muddin tayi magana seka so kaga me wannan muryar

"yi haquri *FADEELA* mun kusa qarasawa gidan Anty maimuna (qanwar mamansu) ,, muna zuwa can shikkenan..


tafiyar mintuna 5 suka qara suka qarasa wani qaton gida duk sun jigata, suka shiga har main falourn, a falourn suka taddata kamar yadda suka saba in sunzo mata ziyara haka fadeela taje ta d'ane ta, tana fadin momy momy, saidai chanji da suka gani daga fuskarta ba kamar in sunzo ba yadda take tarbar su, 


anan suka zauna ta kawo musu abinci da abinsha,, nan safrah ta share hawayenta da fadeela harda iya ma suka soma kwasar garar abinci, 

a bangaren Safiyya kuwa kallonsu kawai take dan farincikin su shine nata ko bataci ba ma ita a haka ma ji take ta qoshi, 

Anty maimuna ta zo ta zauna tace da safiyya


"safiyya ya qarin haqurinmu kuma"

sai lokacin hawaye suka zubo kan fuskar safiyya cike da karyewar zuciya, ta dan dake tareda goge fuskarta tace

"mun gode Allah" , anty maimuna ta dora

"yanxu to meke tafe daku?"

dukka saida sukaji tambayar banbarakwai, banda fadeela wacce ita bama jinsu take ba abincinta take ci,


cikin rashin qwarin gwiwa safiyya tace

"Anty kema kinsan kaddarar data afka mana wanda ba yin kanmu bane, kin sani sarai abbana beyi abinda suka ce yayi ba, Anty bamu da inda zamuje, dan Allah ki taimaka mana anty"


"To safiyya nidai gidan nan ba nawa bane anjima in maigidana ya dawo se muji abinda zece" 


dukkansu shiru sukayi kamar wanda ruwa ya cinye su, mintuna kadan suka kammala cin abincin banda safiyya dako taba cokalin batayi ba, Iyace ta lira da hakan tace 


"safiyya ci abincin mana" dan yake tayi ta dauki cokalin ta soma kai abincin bakinta cike da fargabar abinda ya samesu ze qara samunsu kenan,



bayan sun kammala ta nuna musu dakin da zasu zauna, dakine mai yalwa suka shiga dukkansu fadeela kuwa tana shiga bacci ya dauketa, safrah ma dayake tana fashin sallah tayi kwanciyarta dan ba qaramin jigata sukayi ba, ita kuwa safiyya bandaki ta shige tana hawaye dan jin amsar da anty maimuna ta bata kadai ya isa ya tabbatr mata bazata taimakesu ba, saida tasha kukanta ta koshi sannan ta soma alwala, sanda tazo shafar kai na ga gashinta wanda rabinshi ne safrah takeda amma dukda haka ana mata kallon mai gashi, safiyya kuwa nata har qarshen gadon bayanta kuma baqi ne wuluk sa6anin na safrah da yake ja, sedai takan nannadeshi ne hakan yakesa ake zaton ko acuci tayi ga wanda be santa ba.. Iya kuwa tana kallon duk motsinsu ta rasa meke mata dadi...


bayan safiyya ta gabatr da duk sallolin da ake binta ne ta idar da laziminta ta kalli iya ta gaida ta, iya ta amsa cikeda fara'a sannan tace

"Dan Allah Safiyya ki dena damun kanki kar ki sakawa kanki ciwo, ki tuna yanxu qannenki basuda kowa seke, kece kadai gatansu kece zaki kula dasu, wannan abu daya faru qaddara ce wacce ta riga fata, dukkanmu bamu da ikon chanja komai shikuma Allah ya bimai haqqinshi, dan bazasu ta6a gamawa da duniya lpia ba"

safiyya ta daga idanuwanta masu abin tsoro dan inta zare maka su zaka iya sakin fitsari,

"iya ashe haka rayuwar nan take dama, ki duba yadda ake ji damu sanda muke dashi, yanxu kuma mun zama bola kowa gudunmu yake iya, wai ace har anty maimuna ma, iya a yau gidan enuwa munje kusan 6 amma kowa korar mu yake kan abinda bamuji ba bamu gani ba...

*WALLAHI IYA NAYI ALQAWARIN DAUKAR FANSAR ABINDA AKAWA MAHAIFINA KO NAN DA SHEKARU NAWA NE* "

Safiyya ta qarashe zancen tana zubda hawaye mai quna, jijiyoyin kanta dana idonta duk sun fito,, Iya ta lallasheta kawai dan bazata hanata rama abinda akayi musu ba kuwa,,


"iya yanxu idan anty maimuna ta ce bazamu zauna a gidanta ba ina zamuje?"

safiyyan ta wullowa iya tambayar

"tirqashi", shine abinda iya ta fada dan tabbas basu da gurin zuwa sunsha wahala iya wahala sunga wulaqanci da cin zarafi kala daban daban duk dan basu da komai,, safiyya tayi mamaki sosai yadda en uwanta na kusa dana nesa suka juya musu baya saidai tasan Allah yana tare dasu kuma shine ze rufa musu asirinsu.......



*BAYAN SHEKARU 2*......







             💍 *PAGE 002* 💍


                        


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM



A wannan rayuwar na fuskanci abubuwa kala daban daban a yaune na cika shekaru biyu da barin gidan da mahaifina ya gina shi da guminshi bani kadai bama harda qannena guda biyu,, mun fuskanci wulaqanci a shekaru biyun (2) da suka wuce wanda yayi sanadiyyar sauyawar dabi'una, fuskata ta koma tamkar dare mai matuqar duhu ko nace kogo mai azabar duhu saboda tsabar rashin walwala, yayinda zuciyata ta koma tamkar dutse saboda rashin tausayi, a takaice dai ni *SAFIYYA* na zama wata daban tausayina iya en uwanane....



       * * * * * * * * * * * * * * *


qarfe 4:30 na yamma


gidane dan qarami mai dakuna biyu da bandaki da kitchen se dan qaramin tsakar gida da soro wanda ko tabarma bazaka iya shimfidawa a soron ba saboda qanqanta, sedai ko ina a gyare yake a cikin gidan  kamshin turaren wuta ne kadai ke tashi.


budurwa ce wacce bazata wuce shekaru 18 ba ta shigo cikin gidan dauke da sallama a bakinta, tana sanye cikin pakistan riga da wando ash and black kasancewar hannun rigar dogone dukda shara2 ne yasa tayi rolling dan qaramin gyale, fuskarta akwai kwalliya amma ta danyi fading dan da alama dawowarta kenan, jakarta doguwa na saqale a hannunta kan kafadarta, kafarta kuma tana sanye cikin shoe mai kyau.  yatsanta na hannu sanye da zobe na ado (fashion) guda daya....


*Iya* ce ta amsa mata sallamar wacce take madafa tana qoqarin dora sanwar abincin dare,, shigewa tayi itama daya daga cikin dakunan sannan ta rage kayan jikinta ta dauro towel dan tayi wanka saboda rage zafi...


fitowarta tsakar gida yayi daidai da shigowar wata budurwar wacce akalla ita kuma zatayi kimanin shekaru 23 a duniya, Iya ce ta fito, dattijuwa wacce zatai shekaru 58, murmushi tayi 

"sannu *safiyya* yau kin dawo da wuri"

Iya ta fadi hakan tana kallon wacce ta shigo yanxu,

se kuma Iya ta maida kallonta gun dayar da take daure da towel,

" *safrah* iyayen wanka yau baki dawo da wuri ba"


safiyya ce tayi magana yayinda take qoqarin shiga dayan dakin 

"yawwa Iya sannu da gida" shine kadai abinda ta furta sannan ta shige dakin

safrah kuwa murmushi tayi, 

"iya sannu da aiki bari naje na watsa ruwa dan wallahi yau an sha rana, wai ni ina *Fadila* ? dan nasan yau alhamis babu islamiyya,"

Iya tace

"ai fadila rokona ta dingayi Allah da annabi na barta taje makwabta wai an kunna kallo"

dan murmusawa safrah tayi, sedai a badini murmushi nata yana dauke da tarin bakinciki ne idanun safrah sun dan kawo ruwa tace

"Allah sarki Iya rayuwa kenan...." sauran maganar safrah ta maqale ganin safiyya ta fito da kwandon wanka a hannunta har tayi hanyar bandaki ta shige

binta safrah tayi da kallo, a ranta tunani kala kala har hawaye suka zubo ba tareda ta sani ba

iya ce ta ta6ata

"safrah ki dena kuka, kedai kiyiwa er uwarki addu'a nasan abinda yake ranki..." tun kafin iya ta qarasa zancenta safrah ta shige daki tana kuka (dama safrah da saurin kuka) iya ta bita 

"ya isa ya isa haka", 

safrah ta dan tsagaita

"iya ki duba yadda rayuwa ta mayar min da er uwata, sun maidamin ita kamar ba mutum ba, Iya yanxu anty safiyya bata murmushi sedai in fadila na nan ko kuma *YAYA ARFAT*, burinta ta inganta rayuwarmu nida fadila matsayinmu na qannenta, mune kadai take gani taji dadi, iya kece kadai baki gujemu ba sai kuwa *yaya arfat*, sun tarwatsa farincikin er uwata, iya me tayi musu, alhalin da ba haka take ba"


wasu hawaye masu dumi suka silalo mata iya ta soma lallashi

"ai rayuwar kenan safrah kedai kiyi qoqari kiyi karatu kiyi kudi ku hada kai ku kwato en cinku"

"wannan shine alqawarinmu iya"


Safrah ta fadi tareda kurawa guri daya ido




wani hamshakin falour ne wanda ya kawatu da kayan alatun morewa rayuwa an narka dukiya iya dukiya dan nera tayi kuka, girman falourn kuwa ba'a magana, kujerun falourn milk ne gabadaya, mamallakin falourn ne a zaune kan daya daga cikin kujerun yana sanye da qananun kaya ya dora qafa daya kan daya, yayinda tv din falour ke aiki dukda ba ita din yake kallo ba kasancewar akwai jarida a hannunshi wacce ta rufe mai fuskarshi kasancewarshi mai qulafucin karanta jarida, dogwayen yatsunshi suka tabbatr min da lallai yana da tsayi, yayinda suke sanye da zobuna masu sheki, a wrist dinshi kuma a gogone a daure, masu tsaronshi mutum biyu ne daga dan bayanshi, a can bakin qofa kuma wasu mutanen ne, teburin dake gabanshi kuma shaqe yake da kayan motsa baki, 


wani sanyayyen kida ne ya soma tashi daga daya daga cikin wayoyin dake gefenshi,, maiyi mai hidima ya qaraso tareda miqa mai wayar da take ringing cike da ladabi da girmamawa, a hankali ya sauke jaridar dake hannunshi tareda ajiyewa yayinda kyakkyawar farar fuskarshi ta bayyana wacce babu ko digon baqi saurayine wanda ze kai kimanin shekaru 32 a duniya... base na tsaya 6atawa mai karatu lokaci ba wajen fadin baiwar kyawun da yake dashi ba, na bar mai karatu yayi iya hasashen shi, danko hancinshi ma abin jan hankali ne


a hankali ya karbi wayar fuskarshi babu yabo babu fallasa ya amsa kiran ya saka a kunne....



Aysha b. ce 


Masoya na ina godiya sosai, kuma soyayya daya dazaku nuna min shine ku tayani posting, wannan na samu nayi page biyu amma gaba ba lallai nayi biyu a tare ba....

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Your Ad Spot

Pages