Breaking

Sunday, July 15, 2018

LAMARIN DUNIYA page 02

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺


♥πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *LAMARIN DUNIYA*♥ πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š _(Labarin Zulaihat da Sadiq)_



*_NA:_*

*ALIYU MIKO MUH'D* πŸ‘¨πŸ½‍πŸ’»

*08184427958*

*mikoaliyu3@gmail.com*

*Wattpad:* *MIKOALIYU*
*___*
*THE KING OF WRITER'S* πŸ‘‘



*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
☆We the best ☆


Email:realhausafulaniwriters@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

follow us on facebook


https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

*Insta garam*

https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


**


*_🎢 Hmm.. Sonki ya sani sambatu tamkar naπŸ’• haukace.. Harsun ce na cika Ι“aΙ“atu kan Ι—iya mace.. Fito su ganki domin nasan zasu rikirkice.. Ba kyawu na fuska kaΙ—ai ba harda hali ba rigima! 🎢_*

*_🎢Yayyafin ruwa na sauka.. Ajikina ya sauka.. Gareni baka da tamka.. Duk yanayi ban gudunka.. Tarbiyar da kaimin a so ina al'fahari zana riqa.. Da ido zaku gama juna gaske ne ba tantama!🎢_*

*_🎢Muhalli na baki tuntini zoki zauna a zuciyata... Zuciya Ι—aya Allah massani so domin shi nake miki..🎢_*

*_🎢 Taurarona.. Jagorana Zoka riΖ™e linzamina.. Zancen Ζ™auna mutattauna ranar taro miyi murna... Auren_* *_Ζ™auna shine burina tarko na Ι—ana.. Kin kama tsun-tsun na so gani zan tsindimayi da rigima..🎢_*

*_πŸ’•πŸŽΆMuhalli nabaka tuntini zoka zauna a zuciyata.. Zuciya Ι—aya Allah massani so domin shi nake maka..πŸŽΆπŸ’•_*

*___*




*Ina Al'fahari da ku masoyana Allah ya bar zumunci*πŸ‘πŸ½




*Page-0⃣2⃣*


Tafiyar su a hanya ta Ι—an bata masu lokaci sakamokon wasan da Sa'idu yake ta janta da shi har sai da takai cewa ta kusa kaiwa magriba a hanya, bayan sun dawo cikin gari ne Sa'idu ya kalli Zulaihat a lokacin da kwalla ke yuΖ™urin zubowa daga kuncin sa ya kalleta yace 'yar uwata zan roΖ™e ki wata al'farma guda Ι—aya wacce a duniya bacin mahaifiyata babu wata 'ya mace warda na taΙ“a neman al'farma a gareta sai ke cikin alamun mamaki gami da Ζ™aguwa Zulaihat ta Ι—ago kai tace ina sauraron ka Ι—an uwana wanda nasan a duk duniya bacin kai babu wanda yake Ζ™aunata Ζ™auna ta sai mahaifiyata kuma gashi yanzu Allah ya Ι—auki ranta bani da wani gata wanda ya wuce kai, jin wannan kalami na Zulaihat sun Ζ™asa Sa'idu tausayin Zulaihat matuka kuma yaji Ι—aΙ—in maganar a ransa.. Bacin ya share hawayen sa sannan ya dubeta yace, Zulaihat haΖ™uri shi kawai nake da bukata a gare ki da kiyi.


HaΖ™uri kuma yaya Sa'idu eh tabbas hakane haΖ™uri hakuri akan wa kuma? Rayuwar gidan ku da kuna uΖ™ubar da kike fuskanta kanta na Ι—an wani lokaci tabbas Allah yana sane dake kuma yana kallon ki kisani cewa bawai don Allah baya sonki shiyasa ya barki acikin wannan rayuwar ba tabbas akwai abunda yake nufi a gare ki don haka kada ki kuskura kiyi wasa da wannan jarabawa taki idan kika Ζ™ara haΖ™uri zaki sha mamaki kuma na tabbata idan wannan lokaci yayi zaki tuna dani kuma zaki san cewar gaskiya Ι—aya ce. LAMARIN DUNIYA sai haΖ™uri.


Yaya Sa'idu naji batunka kuma na yarda da wanna kalami naka amma shin meyasa kake min wannan nasiha a lokaci guda kuna a irin wannan guri da babu sirri?


Cikin alamun kaΙ—ai tuwa da nuna rashin jin daΙ—i a tattare da fuskarsa yace, Zulai ba lallai bane fuskin mu su sake saduwa ko kuma kunnuwanmu suji kalamin wani daga cikin mu ba Zulaihat ki sani cewa a daren yau zan bar Ζ™asar nan baki Ι—aya domin yau ne akwani na suka cika na barin wannan Ζ™asa kamar yarda nai mahaifiyar ki al'Ζ™awarin lokacin ina yaro a sa'ilin da zata rasu tamin kashedi kuma ta gargaΙ—e ni da cewar duk wata wuya ko Ζ™unci da zaki shiga a duniyar nan kada in kuskura nace zan, taimakeki wajen kara kanki sannan taimin wasiya da cewar da zarar kin zama burdurwa kin mallaki hankalin kanki kada na kuskura nace zan zauna tare dake ishiga duniya neman arziki kada in wai-waiyi in da kike har sai na zama mai kuΙ—i abun kwatance kuma mai girma a idon mutane idan da rabon sake saduwar mu mu haΙ—u idan kuma sai a can matabbata ina mai fatan Allah ya haskake rayuwar ku daga Ζ™unci da damuwa kuma yaba ku ladan haΖ™urin da zaku riska bayan mutuwata da wannan kalami nake muku ban kwana, nima haka zanso ace kin Ζ™ara haΖ™uri don nasan addu'ar iyaye karΙ“Ι“aΙ“iyace ko da ma agun Allah ne da wannan furuci nake miki Ban kwana" sai kuma, mun sake saduwa na barki lafiya 'yar uwata.

KuΙ—i ya zaro kimanin duba talatin (30) ya miΖ™a mata yace karba wannan shine gadon ki da mahaifiyar ki ta barmiki kafin rasuwar ta ni kuma ban gushe ba wajen anadana wannan dukiya har izuwa wannan kalokacin da na miΖ™a miki ita fatan baki barta ta salwanta ba.

Daga nan bai sake ambata mata komai ba sai kawai ya kada kai ba tare da ya sake juyowa ba yayi tafiyarsa, babu abunda Zulaihat ta iya yi daga cikin lamarin dan uwanta Sa'idu sai kallo dama akwai ranar da zata zo ta raba su da dan uwan ta bata wani bata lokaci ba hawayen takaici da bakin ciki suka soma kwaranya a fuskarta... Tabbas rabuwa tana da zafi koda da maΖ™iyinka kai sai kaji wani abu ya taΙ“a zuciyarka.

Ji take tamkar ta samu wuΖ™a ta hallaka kanta amma idan har ta tuna da wasiyar da sa'idu yayi mata sai zuciyar ta tayi sanyi ta Ζ™ara dan ne ta dag sharrin da sheΙ—an yake nufinta dashin haka dai ta dangana ta Ι—auki ruwanta ta sanya Ι—aya aka Ι—aya a hannu kamar yarda tayi a baya ta soma tafiya duk tsananin yunwar da gajiyar da take Ι—auke da su sun kau babu abinda ke ranta face maganar Sa'idu da shikansa ma aka dai tai ta tafiya har ta Ζ™araso izuwa unguwarsu.


*_Please don Allah kuyi malage da wannan wallahi uzuri ne yayimin yawa amma ku tar dani a page na gaba idan Allah ya kaimu nagodeπŸ™πŸ½_*


*Ina yinku kuna yina*


_Masoya na amana_ ❤

Mrs: *Ali ne* πŸ‘‘


✍🏽

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Your Ad Spot

Pages