💝💝 SO FARUWA YAKE 💝💝
🎀🎀🎀
🎀🎀
💝💝
💝 Love just happens👌🏻
By,, Aysha b (Aeshab)💌
© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
☆We the best ☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
Email: realhausafulaniwriters@gmail.com
Web Page:
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com
Follow Us On Insta_gram
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1
بسم الله الرحمان الرحيم
034
sabon babin shagwa6a khadija ta budewa safwan tunda taga tanada cikin nan,, gashi kuma yana sakata kasala, har makaranta tare suke zuwa yanxu se yaga ta shiga class sannan zai kyaleta,
sanda safwan ya sanarwa su alhaji malam, karkaso kaga murna a tattare da alhaji malam, ba karamin dadi yaji ba, abin yayi mai dadi sosai, ummi kuwa tafi kowa bakincikin wannan abu ita wai kamar ita ta hada zuri'a da er aiki, wannan abu yafi komai 6ata mata rai, duk yadda takeji da safwan dinta yadda en mata ke sonshi da hauka a kanshi, har yanxu ummi ta kasa gano kyawawan halayen khadija wanda yaja ra'ayin safwan,
shirye shiryen dawowa nija sukeyi dansu khadija sun sami hutu kuma yaje checkup dinshi na wannan watan, kullum safwan na manne da khadijanshi tun bataso har ta rabu dashi seyace shi gun babynshi yazo, sedai akwai abinda ke damun safwan saboda yadda suke da khadija yanxu yanaso yaji cewar ta amshi soyayyarshi, dan gaskiya yana bukatar matarshi yanxu, shi abinma har mamaki yake bashi yadda yake hidimtawa wata mace bayan shine en mata kebi, yau shi mace ke wulaqantawa tana ja mai aji, ko iya wannan ma ya isa ya nuna mai bambancin khadija da sauran mata irin su arfa dukda itama arfan yanxune ta zama haka...
a bangaren su umma kuwa su oga sun dawo dan har sun bincika mata inda khadija take kuma sun tabbatr mata tana india amma sun kusan dawowa nija, dan oga ba karamin shu'umi bane yana hulda da mutane daban daban duk inda kake a fadin duniya seya nemoka danshi a gurinshi ba qaramin aikinshi bane, a takaice ma yasan cewar khadija tanada ciki amma be sanarwa su umma ba danshi a ganinshi ba abune da suka tambaya ba kuma beda muhimmanci tunda baya cikin aikinshi,, yanxu su umma jira kawai suke khadija ta dawo,
khadija kuma a nata bangaren tunani yana addabarta, gashi ita ba uwa ba, batada kowa da zataje ya bata shawara, zuciyarta tana fadamata tana qaunar safwan sedai ta kasa amsa hakan kome yasa? oho mata,,, tunda zancen cikin nan ya fara, yadda suke da safwan yake sakata qara sonshi sosai amma hankalinta yaqi kwanciya data amince mai, wannan tunani kan dagula mata lissafi (nikuwa a ganina ba abune mai wahala ba sedai kuma me karatu in ya duba ta fuskar khadija da yadda take bata da wani experience kan zamantakewa tunda ta taso ne a qauye kuma batada qawaye so zata dinga gani kamar safwan ze cutar da ita ne saboda abubuwan da suka dinga faruwa, wanda yaci ace ta gane daze cutar da ita da tuni yayi,,)
sun shirya tsaf sun fito, safwan dama yayi sallama da dr. wajen 12 na rana suka iso garin kano, duk zuwan da khadija zatayi kano setaji dadi sedai wannan karan ta kasa gane meyasa takejin wani bakon lamari a tattare da ita kamar bata farincikin sauka,, driver ne yazo daukarsu dan alhaji malam baya qasar ma, amma yayiwa driver bayanin komai, gidan ummi straight suka wuce, a falour suka tarad da ita ta dora kafa daya kan daya tana karkada qafa, tasha adonta cikin brown less me kyau tana kallon tv din, sallamarsu tasa ta dan juya tana kallon qofar da suke shigowa, ko kallon arziki basu samu ba dan ita har safwan dinma haushi yake bata ko kanme ze wani yi ma khadija ciki, duk haushinshi takeji,, yanayin yadda sukaga ummi yasa kowa yasha jinin jikinshi ba kamar khadija ma,, zubewa sukayi suna kwasar gaisuwa, da kyar ta amsa da lpia sannan ta miqe, "kazo ka sameni a sama" ta fada ta wuce abinta, kallon juna sukayi shida khadija, seda khadija tace ka tashi ka tafi mana, kmar kazar da kwai ya fashewa a ciki ya miqe jiki a sanyaye yana fargabar abinda zeje ya tarar, khadija ma ta tsorata, ta samu guri ta zauna kan kujerar tayi shiru, kawai se wayarta ta soma qara dayake ta saka layin nija dinta, number hafsat tayi appearing kan screen din da murna ta dauka dan tama manta ta,,
sallama sukayiwa juna suka amsa
"kin manta dani khadija ina kika shiga ne haka daga zuwa india an nemeki an rasa" dan murmusawa khadija tayi "haba kawata ya zakice haka kinga yau dinne ko 1 hr bamuyi da sauka ba" "ayya toya gari ya jin dadi"
"Alhamdulillah" khadija ta fada, se suka fara hirar school inda khadija ke sanar mata ai harta fara wata a india ma, daga karshe suka rufe hirar da in hafsat ta samu lokaci zatazo..
safwan kuwa sanda ya hau sama ya samu ummi a falour, ya zauna kenan se ga arfa itama ta fito daga dakin se cika take tana batsewa,, wani haushinta ya kamashi, yanxu meyasa ummi ta kira mai arfa ne,
zama arfa tayi kusa da ummi yayinda safwan ke zaune a qasa ya sunkuyar da kanshi
"so nake ka fadamin meya hadaka da eruwarka?" ummi ta tambaya tana kallonshi babu fara'a,,, shi safwan yanxu duk ummi ta chanja mai,, yadda yake da ita amma lokaci daya ta sauya,
"ummi babu abinda ya hadamu" se arfa ta chafe tana fadin "wlhy ba wani nan ummi tunda yayi rashin lpiar nan mayyar nan (dayake haka take cewa khadija) ta asirceshi wayasan me tayi mai ta hadamu alhalin da ba haka yake ba kuma fa cewa yayi ze saketa ai amma kinji dan cin mutunci wai har cikine da ita nikuma yasan munyi alkawarin aure dashi..." se kuka yaci qarfinta,,
"yanxu safwan yaudara kafara kenan kome?" ummi ta fada tana jawo arfa jikinta tana lallashi, kace kana sonta shine kaje kayiwa wata ciki bayan kasan kunyi alkawarin aure da arfa,, "ummi ni khadija nakeso itakuma arfa ai eruwata ce alqawarin aure kuma wannan da kenan sanda bana gane bambamci tsakanin aya da tsakuwa...." bugeshi umma tayi da qafa,, "shashasha har ka isa kazo gabana kacemin wannan yarinyar kakeso, to wallahi maza ka sauya ra'ayi ni mahaifiyarka ina umartarka kaje ka sanarwa alhaji malam kanaso a daura maka aure da arfa, inba haka ba wallahi kaji na rantse maka sena sa6a maka, inba haka ba kuma ka nemi wata uwar bani ba kuma sati daya na baka a fara shirin biki..." ta qarashe zancen tana jan arfa daki suka barshi nan zaune kamar soko, dafe kai yayi yana kiran sunan Allah, wannan wanne irin abune? meke shirin faruwa dashine? shi khadija yakeso, miqewa yayi ya sauka hankalinshi a tashe, dama driver su yake jira dan alhaji malam ya gyara musu wani gidan amma wannan na safwan dinne be qarasa aikinshi ba se cikin kwanakin nan aka qarasa shine alhaji malam yace sukoma can tunda an gama komai,
fitowarsu kenan, khadija kuma se kallon safwan take wanda tasan tabbas akwai matsala, yayi daidai da shigowar hafsat, sunyi murna da ganin juna sosai, suka gaisa da safwan nan khadeeja ke sanar da ita ai gida ma zasu tafi dan haka tazo su wuce ba musu suka shiga suka wuce,,
abin mamaki unguwarsu daya da hafsan, unguwa ce ta masu nerori, kaf unguwar akwai wani gida a bakin layin da babu irinshi a unguwar dan gidane tamfatsetse ko baka shiga ba kasan bana qananun mutane bane naira ta zauna kai da ganin tsawon ginin ma ya isa tabbatar maka da hakan, khadija har suka wuce gidan tana kallonshi, gida hudu ne tsakaninsu da wannan katon gidan da ake kira da *gidan Alhaji* daga gidansu khadija kuma tafiyar kadance se gidan hafsat,
(nasan me karatu ya gane gidan Alhaji shine gidansu umma), sam wannan sabuwar unguwar bata kwantawa khadija a rai ba..
gidan safwan yanada kyau sosai babu bene flat ne, in short two falours ne da 4 bedrooms manya sosai se wani katon kitchen kusa da dining, kowanne room da toilet, bakadan ba gidan yayi gaskiya dan ko furnitures ma sun isa abin kallo, komai a shirye yake, hafsat se santin gidan take,
safwan falourn shi ya wuce itakuma suka wuce kitchen itada hafsat, dan safwan yace ta kyale zeyi ordering amma taqiya yayi yayi amma taqi dan haka ya rabu da ita musamman yadda ummi ta dagula mai lissafi yana buqatar ya kadaita yayi kyakkyawan tunani, hira sukeyi sosai da hafsat da khadija inda hafsat take bata labarin ai sun fara shiryawa da mijinta dan addu'ar da khadija ta bata ta dagewa abubuwa suna tafiya daidai.
No comments:
Post a Comment