Breaking

Sunday, August 5, 2018

LEEKITAN ZUCIYA page28 (The End)

`☆´-`☆´-☆“˜•☆•¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ LEEKITAN ~ZUCHIYAH
*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-☆“˜•☆•¸☆“☆ª☆_☾`☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
      A true life story
April.. 2018.. *Viawattpad@rahamanalele*

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
realhausafulaniwriters@gmail.com
☆page 28☆ qarshe😍

Lumshe idanta NUFAISAT tayi cikin jin wani iri ajikinta haka...
Shima ADAMS d'in yaji hakan dan haka saiya zaunar da ita kan kujera cikin rikicewa yake qare mata kallo da cewa.. "Koma miye zai faru ina rokwan Allah daya barni da matana....
Murmushi NUFAISAT tayimai hawaye ya qara zubo mata da cewa.. "Na tsinci kaina dasan binka asibiti yau mijina. Dan Allah karkace aa. Ina san kawai naganni dakai ne. Saboda naji wani mafificin tsoro araina yanxu kamar idan katafi wani abu zai faru dani..
  Kallo d'aya zakama ADAMS kagane ya qara rikicewa.. Dan haka tashi yayi da shiga bedroom nata ya d'auko mata gyalanta yayafa mata da cewa. "tashi muje matata.. Dan nima ayanxu yanda nake ji araina bazan iyama tafiya nabarki cikin wannan yanayin ba..
Kan tabashi amsa kiran YUSUF ya shigo wayarsa.. Cikin sauri ya d'auka inda Yusuf d'in yake cemai dan Allah ya tawo asibiti da sauri yanxu ya kawo Hajjiyansu yau kam jikin nata ba sauqi.. Dan har aman jini takeyi.. Amma Dr Ibrahim ya bata temakwan gaggawa har tasamu bacci. Amma duk da haka Shidai kawai yazo dan yafi gane aikinsa fiye dana Dr Ibrahim d'in..
Rintse idansa ADAMS yayi dacemai Gashi nan zuwa..

Haka suka fito masu tsaransa suka bud'e masu kofar mota suka ficce sam kotakan MUSLEEMA Adams baibi ba..
Dan haka MUSLEEMAN najin fitarsu tashiga wanka sama sama da d'aukar y'arta little NUFAISAT tayafa gyalanta tafito da cema direban gidan yabi mata bayansu Auntynta NUFAISAT
ina yasan inda suka nufa. Yace mata ba mamaki asibiti suka nufa. Tace mai to maza yakaita gunsa...

Dake ADAMS yana baya direbansa ne me tuqasu dan haka NUFAISAT na jikinsa tayi lef da ita kamar matacciya..
ADAMS yana jin wucin zafin da jikinta yakeyi.
Nan ya fahimci zazzab'i ne yake shiga jikin nata..
Ai ba shiri ya d'ago da fuskarta arikice yake cewa.. "NUFAISAT ke NUFAISAT wai meyake daminki ne.. Shuru tamai dana me lumshe ido da bud'ewa kad'an kad'an..
  Iya rikicewa ADAMS fa ya rikice.. Dan haka cikin tsawa yake cema direban nasa ya qara gudu..
Sam NUFAISAT baki ya rufe dan bata cewa umm bare um um..

Suna isowa ya kwantar da ita kan d'aya daga cikin kujerun office d'in nasa. Yusuf Yace mai.. "Lafiya meya sameta. "Wallahi YUSUF yanxu fah kamar wasa zazzab'i ya kamata. Bara na kira Dr Aryan ya duba min ita. Nan ya kira Dr Aryan yahau duba masa ita...
Aiko Dr Aryan ya gane zazzafan zazzab'i ne ya shigeta nan take..
Dan haka suje su kwantar da ita kan gadan asibitin dan bata cikakken temakwan daya dace da ita..
 
Nan ADAMS ya d'auki NUFAISAT dan kaita d'akin dake da gado. Aiko yana kwantar da ita sai yaga kamar bata numfashi.. Arikice yakai kunnansa setin qirjinta dan yaji tana numfashin  ko batayi..

Ai dai jin ADAMS yaji bata numfashi. Dan haka cikin wani yanayi me tafe da tashin hankali yahau girgizata yana cewa.. "NUFAISAT ke NUFAISAT ke matata.. Dan Allah kitashi.. Dan Allah na roqeki daki tashi pls.. NUFAISAT NUFAISAT. Haba NUFAISAT..

Ina shuru NUFAISAT bata da alamar amsa ma ADAMS...
Dan haka saiya saketa yaja da baya hawaye na zubo masa tunaninsa tamace ya kalli Dr Aryan da YUSUF dake waje jikin window yana Kallan abubuwan da suke faruwa yace dasu... "NUFAISAT tatafi Tamutu ta barni. Zan iya rayuwa kuwa.. Yana fad'in hakan ya zube qasa sumamme agun...
Nan Yusuf ya shiga d'akin da matuqar rikicewa ya temakama Dr Aryan suka sashi kan wata kuje dake d'akin..  daqer da sid'in goshi Dr Aryan yasamu ADAMS ya farfad'o.. Lokacin ko a akan idan NUFAISAT ya farfad'o dan haka suna had'a ido tasakar mai murmushin yaqe da cewa.. "Na d'auki kwanaki uku mijina ina jin wani yanayi ajikina da fad'uwar gaba. Hak'ik'a MUSLEEMA ita taji abinda taji yau aranta mijina. Ina san rayuwa daku amma hakan bazai yuhuba. Saboda lokacina yayi. haka dole natafi na barku. Takai qarshen zancen nata da zubo da wani hawaye me d'umin gaske. Sannan tacigaba da cewa.. Nagode ma Allah dayasa kakeda MUSLEEMA mijina.. Ina san kariqeta amana ka....
ADAMS bai bariba ta qarasa zancenta ba!!! ya katseta wajen cewa.. "Waya gaya miki idan babu ke zan iya rayuwa.. Banyi zatan abinda nake gaya miki akullum zai kasance awannan ranar ba.
Nima gasu sunzo da fararan kaya suna san d'aukar rayuwata NUFAISAT.
Dan haka Ina yima MUSLEEMA fatan alkairi a rayuwarata..  dan zatayi rashi biyu a lokaci d'aya..

MUSLEEMAN na jikin window tana jinsu tana kallan abunda yake faruwa dan tun sa'adda YUSUF ya shiga d'akin tafahimci ba mamaki kosu NUFAISAT d'in suna ciki. Danta duba office d'in ADAMS baya nan.
hakan yasata isowa wajen da tsayawa gurus  jikin windown d'akin. Ganin NUFAISAT kwance ADAMS kwance...

Qara tsaida kallanta NUFAISAT tayi akansa.. Tace. "Zata zama abin tausayi mijina. Ina san MUSLEEMA tasamu Farin ciki me d'orewa. Takai qarshen zancen nata da maida kallanta zuwa ga MUSLEEMA wacce fuskarta tawanku da jiqewar hawaye. Sai Kawai NUFAISAT ta sakar mata murmushi da cewa La'ilaha'illallahu-muhammadarrasulullahi-sallallahu a laihiwasallam. Tana fad'in hakan ADAMS ya rintse idansa da Kallan Yusuf yace.. "Kagani tatafi ko. Kamar yanda tatafi haka kaima zaka tafi. Ina rokwanka da Allah daka Auri MUSLEEMA kabata kulawar data zarce wacce nake bata. Dan nima... Bai qarama YUSUF zancen ba..  ya b'ige da cigaba da faɗin.. La'ilaha'illallah muhammadan rasululla sallallahu'alaihiwasallam.

"NUFAISAT tatafi.. ADAMS abokina wanda ya zama d'an uwa gareni abokin hira abokin wasa da dariya. Abokin kasuwanci na. Me gaskiya me amana me kirki. Wanda yasan abinda ya dace ya bita.. Yusuf ya fad'i hakan da zubewa qasa sumamme...

Aiko MUSLEEMA batasan sanda tayi wurgi da little NUFAISAT ba... Ta kwalla qarar da duk asitin sanda suka jita... Hankalin kowa yayo kanta..
ALLAH yaso wata ma'aikaciyar wajan na tsaye gefe ita ta cab'e little NUFAISAT d'in amatuqar tsorace dan jifan da MUSLEEMA tama little d'in bana wasa bane...

Da wani shegen gudu MUSLEEMA tafad'a d'akin tarasa kan wazatayi cikinsu.. ADAMS ko NUFAISAT.
  Ai kawai sai tayi kan NUFAISAT... Fad'i take.. "Aunty dan Allah kitashi.. Dan Allah Dan annabi Aunty kitashi.. Aunty kinyimin alqawarin bazaki tafi ki barni ba. Kinyimin alqawarin kina tare dani.. Na shiga uku ni MUSLEEMA. Tafad'i hakan da komawa kan ADAMS tana meci gaba da cewa. Ya ADAMS kaima katashi. Dan Allah Dan soyayyarka da manzan Allah katashi kacema Auntyna tatashi muci gaba da rayuwa.. Wallahi ina sanku ina qaunarku ina fatan qare kowace rayuwa daku..

Kuka MUSLEEMA take bana wasa ba. tana zuwa wajen NUFAISAT tajijjigata taje wajen ADAMS ta jijjigasa tana rokwansu dasu tashi suci gaba da rayuwa..

Kaf doctors d'in asibitin da ma'aikatan  asibitin ba wanda bai tausayama MUSLEEMAT ba...
  Sannan sun tsinci kansu da mummunar fad'uwar gaba da suka fahimci DR ADAMS LEEKITAN ZUCHIYA ne da matarsa tafarko NUFAISAT sune suka rigamu gidan gaskiya. Anan wasunsu masu raunin zuciya suka fara kuka wiwi... Suna fad'i dole MUSLEEMA ta shiga tashin hankali dan sunfi kowa sanin waye ADAMS.  Haka suna samun labarin matarsa NUFAISAT da kirkinta da haƙurinta kamar yanda duk abinda kakeyi idan mutane na kanka....

Aqarshe dai bayan Dr Aryan ya samu daidaituwar numfashin YUSUF sai yasa ma'aikatan wajen dasu kaisa wani d'akin. Kana ya kalli MUSLEEMA da zubar hawaye dan mutuwar ADAMS d'in tashigesa sosai shida matar tasa NUFAISAT.. Cikin wani hali ya kama hannun MUSLEEMA da cewa "kiji hak'uri MUSLEEMA.. *Amma kin rasa NUFAISAT da ADAMS rasawa irin wacce ba'a dawowa*

Tsayawa cak MUSLEEMA tayi da kallansa cikin matuqar qarin shiga razana tace.. "Da gaske... D'aga mata kai yayi alamar tabbatarwa... Aiko tana ganin hakan tafad'i qasa luuuu sumammiya...

Mahaifan ADAMS
Mahaifan NUFAISAT
Mama Mahaifiyar TAUDHAT
YAWO
Y'an uwa da abokan arziqi
Jama'ar gari..
Ba wanda bai zubda hawaye akan mutuwar ADAMS da NUFAISAT ba..
Mutanan azziqi.. Masu gaskiya da amana. Masu san mutane. Masu ruk'o da addini. Masu yarda da qaddara..

   (Ina san nidake dakai me karanta wannan littafi nawa na LEEKITAN ZUCHIYA muyi koyi da kyawawan halaye irin nasu.. Dan muyi mutuwa irin tasu. Irin mutuwar da kowane musulmi yake so. Wato cikawa da kalmar shahada. Bacin hakan jama'ar gari da yan uwa suyi kukan rashinmu. Suta fad'in alkairin mu. Suna binmu da kyakkyawar addu'a irinta fatan alkairi agaremu.)

Ammi da Dady sunyi kukan rashin ADAMS da NUFAISAT kamar ransu zai fitta..
Haka mommy na NUFAISAT da Dadynta da ƴar uwarta Zainab sunyi kukan rashinta kuka bana wasa ba..

Haka Yusuf bai tab'a tunanin zai rasa ADAMS nan kusa...
Dan qaunar ADAMS yake har cikin b'argwansa..
Komai jiyayi ya tsaya masa cak dan ganin yayi babban rashi arayuwarsa.
   Ya saka a zuciyarsa zai rayuwa da MUSLEEMA rayuwa irin ta gaskiya da rukwan amana..

Haka MUSLEEMA ta bala'in fitta daga harcinta ganin rashinsu da tayi.
Ta kamu da ciwan ZUCIYA dan akwalla ya ibeta shekara d'aya kafin aka samu kanta da lafiya..
Kullum tunaninta YAYANTA ADAMS da AUNTYTA NUFAISAT sun tafi sun barta...
Ni akayima mutuwa ba kowa ba. Hakan take fad'i dazaran an sakata agaba dan taci abinci ko ana mata fad'a kan tatsaida tunaninta...

Itama Haneepha shekara biyu tsakani tabi bayan NUFAISAT da ADAMS.. Sakamakwan amai da gudawa da tayi....
_________













************************
Dake Yusuf ya saka aransa zai rayu da MUSLEEMA zai aureta. Sai kawai yaji aduniya ba macen da yake so kamar ita..
Dan haka bayan rasuwar Haneepha da wata biyu yaje gun Ammi  yace mata shifa yana san a d'aura masa Aure da MUSLEEMA..
   Lokacin MUSLEEMAN tana falan alokacin da yake maganar..
Dan haka Ammi tace mata to taji abinda Yusuf d'in yace shin ta'amince..
Kallan Ammi tayi hawaye ya zubo mata da cewa.. "Wallahi na amince tun sanda Ya ADAMS  yace mai ya Aureni..
Murmushi Ammi tayi da sunkuyar da kai tashare hawayenta dan bata san taji an ambaci ADAMS d'in.. Yanxu yanxu sai qewarsa ta dameta..

   Daurewa YUSUF yayi da qarasa wajen MUSLEEMAN ya share mata hawayen..
Da cewa.. "Gobe nake san a d'aura mana Aure Babyna..
Kallansa da sauri MUSLEEMA tayi dan aduniya bata ba mance duk wata kalma da ADAMS ya kirata dashi....
Dan haka Ahankali tace.. "Ko yanzu ne INA san a d'aura Ya Yusuf..
Qara share mata hawayen yayi da fad'in.. "Kin tabbatar..
Da sauri ta d'aga masa kai alamar tabbatarwa..

Saiko ya tashi da kallan YAWO yaci gaba da cewa. "Zamma Dady magana yanxu YAWO. Tunda gobe jumma'a ne za'a d'aura Auran namu bayan idar da sallar jumma'a.. Dan Allah YAWO kar kibi tasu Ammi kan saisun sharyamin ita kafin akawota. Kawai idan dai dare yayi  akawomin ita haka. Danna shirya mata komai.. idanko kunyi zanzo da kaina na d'auki abata... Yana fad'in hakan ya ficce daga falan ya nufi wajen shaqatawar gidan dan ganawa da Dadyn..

   Murmushi ammi tayi cikin matuqar qaunar YUSUF.. Dan tunda suka rasa ADAMS ya qara shige musu yana nuna musu idan sun rasa adams ai suna dashi shi da Salim..
Wannan abu yana yima Ammin dad'i..

Haka YAWO tasa ammi tasaka aje wajen masu saidai maganin gargajiya anemo mata wasu saiwa ta had'ama MUSLEEMA maganin manta da bazawa kake tare. Kawai kalleta a budurwa..

Aiko nan Ammi tasa y'an aikinta sukaje suka samoma yawo duk abinda take buqata..
Sannan ta daka na dakawa tabada na dafawa a dafa mata..

Nan tahad'ama MUSLEEMA me zafi.
Ita kanta MUSLEEMA duk da a ranar tafara amfani da had'in amma sanda taji canji ajikinta..
YAWO fad'i take dama saboda y'ar albarka NUFAISAT naqi yimiki had'in mallakar miji. Saboda nasan idan nayima NUFAISAT d'in haka ban kyauta mata ba. Amma yanxu tunda Allah ya d'auke su Yusuf ya shiga uku..
Murmushi MUSLEEMA tayi Kawai tana qara tuna NUFAISAT da mijin nata ADAMS..
Nan hawaye ya zubo mata. Itama YAWON hawayen ne ya zubo mata tayi saurin sharewa wai dan karta qara karyarma da MUSLEEMAN zuciyata..

Aiko a washe garin ranar aka d'aura Auran YUSUF da MUSLEEMAN..
Auran daya tara manyan mutane.. Dan abokan takar YUSUF da ADAMS ba qaramin qarama YUSUF d'in Farin jini tayiba agun jama'a.. Hakan yasa aka san YUSUF d'in kamar yanda aka san Adams d'in..
Haka kuma kunga Dady ne yaba YUSUF d'in Auran MUSLEEMAN
Wannan yana d'aya daga cikin abinda yasa Auran ya samu Albarkan matane masu mugun yawa..

Aranar ko aka kai MUSLEEMAT gidan YUSUF.. Gidan da YUSUF ya d'au shekara da shekaru yana tsari akansa...
MUSLEEMA tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fitta.. Sakamakwan tunawa da tayi ashe zamanta da ADAMS da NUFAISAT na d'an wani lokaci ne..

Kafin akaita gidan sanda YAWO tace mata karta kuskure tabari YUSUF ya tare da ita awannan rana tadai bari sai bayan tagama shanye maganin tunda na sati d'aya ne..
  Toh MUSLEEMA tace mata sannan suka mata nasiha sosai aka kaita gidan YUSUF d'in..

Salim qanin ADAMS ne kawai ya rako YUSUF d'in gidan nasa.. Dan yanxu shine wanda YUSUF d'in ya yarda daya shiga al'amuransa.. Kasancewar yayaba da Hankalinsa

Tsiya Salim ya shiga yima MUSLEEMA akan wai takula mai da yayansa akaro na biyu kamar yanda takula mai dana farko imba haka ba zai hukuntata.. Murmushi Kawai MUSLEEMA tayi kanta na cikin mayafi kamar dai yanda amarya me kunya takeyi idan ankaita d'akinta..
Bayan Salim d'in ya tafi kulle makeken gidan nasa YUSUF yayi da dawowa gurin MUSLEEMAN.

Ahankali ya d'ane gadan  da yaye mata mayafin kan nata yana cewa.. "Haba Babyna. Wannan rufe kai haka aisai zafi ya illatarmin dake..
Murmushi tasakar mai..
Saiya kama hannunta taji wani zirr shima yaji amma yayi fuskar daci gaba da cewa.. "Mu biyu iyayanmu suka Haifa Baby. Daga ni sai qanwata..
Ina matuqar santa da yawa dan haka ina san kema ki sota dan Allah da gaskiya dan yanzu bata kowa saike.. Kinga Hajjiyanmu me kula damu bata nan. Tabi bayansu ADAMS.. Dan Allah matata karki saka wani abu aranki akan qanwata wanda zaijamin matsala dake..
Ina sanki MUSLEEMA Sannan ina san qanwata.. Ina san kizama uwa agareta tun daga yanxu duk da cewar zama ta iya girmanki Kinji..

Qara kafeshi da ido MUSLEEMA tayi da cewa.. "Wallahi zan rayu da qanwarka lafiya da gaskiya da amana har izuwa ranar da zamu kaita gidan mijinta kai har qarshen rayuwarmu mah. Dan banci karo da wani mugun hali ba azamana da kakata YAWO. Sannan na qara samun wata tarbiya agun Auntyna NUFAISAT.. Haka na samu adalci aso tsakanin zamana da YAYANA ADAMS.. Ina tabbatar maka bazakayi dana sani azamana dakai ba..

____YUSUF ayanxu ya girma sosai dan zaikai shekara talatin da tara ko arba'in a takaice.. Amma idan ka kallesa zakayi tunanin d'an ishirin da takwas ne. Saboda yanda Hutu yake tare dashi sam bashi da wata matsala a rayuwarsa..
Yana matuqar buqatar mace me Hak'uri me kyau wacce tatara duk wani abu da namiji yake buqata agun mace..
Sannan yana buqatar mace shagwabb'iya wacce tasan salo kala kala na shwagwab'ar...
Tunda ADAMS ya mutu YUSUF ya tabbatar MUSLEEMA tatara dukkan way'annan abubuwan da yake so agun macen Auransa____

"Yauwa Babyna nagode sosai da bani Wannan tabbaci da kikayi..
Ina san yanxu kije kiyo alwala muyi sallar godiya ga ALLAH...
Cikin sauri MUSLEEMA tace.. "Bana sallah ina al'ada..
Waro ido YUSUF yayi cikin damuwa yace.. La'ilaha'illallahu..
Murmushi MUSLEEMA tasakar mai da cewa.. "Muhammadan rasulullahi sallallahu alaihi wassallam.
Meya na saurin sakar salati haka.
  "Baby bazaki gane ba. Ina cikin wani hali yau. Wallahi buqatarki nake da gudu...

Murmushi tayi da fad'in.. "Kaga dama fa wasa nake maka duk da dama YAWO tace min wai... Saita rufe ido da hannayenta taqi qarasawa.
Murmushin jin dad'i yayi da zare hannuwanta daga fuskar tata Yakai bakinsa cikin nata ya fara aika mata dame zafi. Saura kad'an ya shid'ar musu da ƴar mutane.. Yadai barta sun gabatar da sallar godiya ga Allahn..
Yayi mata tambayoyi akan addini. Ta bashi amsa gamshashshiya..
   Kana ya ciyar da ita abubuwan da kowane ango yake ciyar da amaryarsa adaidai Wannan lokacin. Wato kaza da madara.. Kana ya fara b'ata tunaninta bayan ya d'auketa ya kaita shashinsa..
Nan ya fara Sarrafata kamar na'ura...
Saidai fa qarshen tafiyar kuka YUSUF yasakarma MUSLEEMA da girmansa yana harkar yana godema ADAMS daya bashi wasiyar Auran MUSLEEMAN..

Itama kukan take mai dan taci wiya ba d'an kad'an ba. Tayi qoqari ma dabata sume masa ba. dan sosai Yusuf ya juye mata abubuwan daya d'auki shekara da shekaru yana tattalinma wacce taci nasarar mallakarsa..

Washe gari bayan yadawo daga masallaci daninta yayi zaune a gefan gado da alama fitowarta kenan daga wanka...
Haka ya durgusa a gabanta da kama hannuwanta yace da ita.. "Wallahi Babyna ban tab'a tunanin dake zan faro rayuwa ba...
"Nima haka mijina. Ban tab'a tunanin zanyi rayuwa dakai ba..
  "To yanxu ya jikin naki
"Da sauqi kawai zance maka mijina.. Dan kasan ka juye min da yawa..
  Murmushi yayi da fad'in.. "Yanxuma zan qara juye miki dan bana jin zan iya dena juya miki idan har zanyi ido hud'u dake..
  "Wayyona Allah wallahi Ya YUSUF zaka kashe matarka nan kusa..
  "Idan na kasheta nayi rayuwa dawa..
"Toh kawai kadaure kana juyewa bayan kwana uku uku..
"Wannan ne kuma bazan iya.. Tukunna ma!!! Gayamin.
"Me kakeso kasani mijina..
"Lokacin da kike tare da Adams yana barinki har na tsawan kwana uku...
"Toh ai lokacin mu biyu ne. Kaga dole na dinga samun hutu..
"Toh shikenan zan qara tabiyu kawai dan kidinga samun hutun..

"Ai mijina kishiya idan irin Auntyna ce ina santa ina qaunarta har agidan aljanna.
Magana ta gaskiya ayanda najika adaran jiya bana fatan ka kahad'a da wata y'a mace dan tazama kishiya agareni..
Zanji ba dad'i sosai araina idan taji abinda naji akanka daran jiya..
  Dan Allah mijina kabarni na rayu dakai ni d'aya.. Badan ina qin kishiya ba. Saidan bani san irin TAUDHAT datasa AUNTYNA kuka da YAYANA.

"Idan ko haka ne. To ki'iya ibewa idan na juye miki. Zan rayu dake ke d'aya babu qari..
Wallahi tunda nake arayuwata ban tab'a san wata y'a mace kamarki ba MUSLEEMAT.. Kuma hakan ya farone daga lokacin da ADAMS ya danqamin wasiya akanki. Sannan na qara jin hakan a daranmu na jiya...

Murmushi MUSLEEMA tayi da cewa.. "Nagodema allah dayasa kaine kazama miji agareni akaro na biyu..
Saboda nasan zakaji da komai nawa. Ina baka tabbacin baka da matsala dani dan sai yanda kayi dani..
Sannan nifa Har na kwad'aitu dakata juyewa akowane lokaci dadai kamin kishiya..

Murmushi yayi da sakar mata kiss yace "Bayan ji dake har da ƴaƴanki bazan bari suyi kukan rashin mahaifinsu ba. Dan qaunar ADAMS ajinina yake... ALLAH ya raya min Khalit da Kahlil & Rahma da little NUFAISAT.. yakai qarshen zancen nasa da tashi ya tasar da ita dakai hannunsa ga ware towul d'in dake jikinta.. Aiko cikin sauri ta rungumesa wajen shigemai da cewa.. "Ya dace kidena karanta labarin namu AUNTY RAHMA.. Dan kinji sirrinmu da YA ADAMS.. Yanzu ina rokwanki daki bar mana namu sirrin nida YA YUSUF haka....
Qara rungumeta YUSUF yayi cikin so da qauna yace.. "Barta kawai my Baby. Kedai bani nutsuwa nasamu kwanciyar hankali Kawai..
D'ago da fuskarta tayi zuwa ga kallansa takai bakinta cikin nasa bayan ta aika masa da zafi. Tace zan baka dukkan Farin ciki mijina...
Saurin d'aukarta yayi niyar Kwantar da ita.... Sai kawai ta dafe qirjinta daci gaba da cewa wayyo ZUCIYATA..
Arikice YUSUF ya kalleta da cewa.. "Me yadami ZUCIYAR..
Tace "zafi take min yanzun nan..
   Da matuqar tashin hankali yace da ita... "Dan Allah ki rufamin asiri dan  LEEKITAN ZUCHIYAN ya mutu...
dariya MUSLEEMA tayi da dukan qirjinsa tace... "Toh kazama shi mana..
Yace. "Hmm Amma dagaske babu ciwan zuciyar ko..
Gyad'a masa kai tayi da cewa "Kwantar da hankalinka mijina idan ina tare dakai bani ba ciwan ZUCIYA.. Bare mufara tunanin inda zamu samo *LEEKITAN ZUCHIYA...

Alhamdulillah

*Ni Rahama Nalele Auntyn luv nasan dacewa na b'ata tunaninku*😍

Fatan Allah ga MASOYA LEEKITAN ZUCHIYA
Ina tare daku akone yanayi da kowane lokaci..

Amatsayinku masu makaranta Wannan littafi LEEKITAN ZUCHIYA.
Miyafi birgeku awannan littafi
Miyafi saku nishaɗi
Meyafi baku dariya
Meyafi b'ata tunaninku
Meyafi tafiya da tunaninku
Meyafi baku tausayi
Meyafi b'ata muku rai..
Wata jarumace tafi birgeku
Wane jarumi ne yafi birgeku
A cikin ƴaƴan rajuman wa kukafi so..
Shin rahama Nalele tabaku zafi har kun iya abewa😍😍😍

Alhamdulillah nagode ma Allah daya kaini qarshen wanga novel lafiya..

Dan Allah sister n brothers duk wanda a tsinci kansa cikin wani yanayi acikin dukkanin littattafaina ina rokwansa rokwanki daku yafemin.

Allah ya qarama marubuta y'an uwana masu bin wannan noven nawa basira da fasaha..

Y'an mata way'anda suka karanta ina muku fatan samun mazaje na gari

Haka matan aurema ina muku fatan Allah yasa mazajenku su soku fiye da yanda ADAMS yaso NUFAISAT fiye da yanda YUSUF yaso MUSLEEMA..

Na sadaukar da wannan littafi nawa ga dukkanin way'anda suka so shi.. Dan haka idan ya miki ina jiran comments daga gareku😍😍😍😍😍

1 DAGA WASA ƘARAMAR MAGANA TAZAMA BABBAH

2 YA FARU AKAN KAI NAH

3 MATAR ƳAƳANA

4 MATAR KAMAL

5 HAYATUDDEN

6 AURAN DA A ƘAUYEN FAGO

👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻👆🏻SUNE MASU FITOWA DA IZININ ALLAH
INA KUMA ROKWAN ALLAHN DAYA BANI DAMAR RUBUTA MUKU SU CIKIN LAFIYA NA ƘARE DA NASARA.

Yanxu naku zanyi y'an mata.👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻

By AUNTYN kamar yanda kuka rad'amin😍😍😍luv u 🙅🏻‍♀.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Your Ad Spot

Pages