πΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊπΊ
♥πππππππ *LAMARIN DUNIYA*♥ πππππππ _(Labarin Zulaihat da Sadiq)_
*_NA:_*
*ALIYU MIKO MUH'D* π¨π½π»
*08184427958*
*mikoaliyu3@gmail.com*
*Wattpad:* *MIKOALIYU*
*_______________________*
*THE KING OF WRITER'S* π
*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπ*
☆We the best ☆
Email:realhausafulaniwriters@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com
follow us on facebook
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
*Insta garam*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1
*Nasiha:*
ππ *_ABUN DUNIYA MAI KAREWA NE YA KU Ζ³AN UWA MUSULMAI ZAN SO KU GANE HAKAN IDAN HAR KUN FAHIMCE NI KAIDA KEDAI KAWAI KI KASANCE KIN/KA BAUTAWA ALLAH KA DOMIN KA SAMU RABAUTA DUNIYA DA KUMA LAHIRA...._* ππ
*GARGADI:*
```Ba'a yarda wani, ko wata su sarrafa wannan Rubutun ba ta ko wacce siga ba tare da amincewar mai shi ba ko kungiya don haka a kula a kiaye```
*_Har ila yau kungiyar mu mai al-barka ban manta da ku ba a wannan tafiya Allah ya bar zimunci_*
_RAHAMAT MUH'D RUFA'I NALELE:_
*_Allah Kara basira ya kuma bad a sa'a ππ½_*
*INAIWA AL-UMMAR MUSULMI BAKI DAYA BARKA DA SALLAH.*
_Allah ya mai maita mana_
_Page-_ 0⃣1⃣
πΈauri take tsulawa mai matukar ban al-ajabi surutu da mitar da take ya nuna alamar cewar tabbas ranta a bace yake, saboda tsabar saurin da take zabgawa na wuce misali yasa bata wani jima tana tafiya ba ta isa izuwa kofar wani babban gidan kasa wanda da ganin alamu gidan manyan mutane ne wanda suka jima a kauyen babu sallama bare kara ta make kofar gidan ta shige ciki cikin fusata.
Karar buge kofar gidan da tayi ne yasa gabaki Ιaya ilahiran mutanen gidan suka firgegita kowa ya fito waje ganin abinda suka fito suka gani a waje ya sasu fisata ainun gabaki Ιaya suka ja tsaki ko wa ya saita izuwa komawa Ιakin sa babu wani abu da ta iya cewa in banda kutuntumo ashar, mai karfi sannan ta biyo bayan ashar Ιin dacewar: Shegu 'yan iska malalatan banza da na wofi wai ace tsabar wulakanci daga fitata unguwa sai kawai a karbi kuΙin girki na al-halin dukkan ku kunsan dacewar yau ranar girki na ce.
Allah da girma yake yo inbanda abun ta tunda har taga cewar tayi surutan da masifar babu wanda ya mata kallon kirki ballantana ya dubeta mai makon ta tsagaita sai ta cigaba da kutuntuma musu ashariya.
Haka dai tai tayi har ta gaji ta koma Ιaki ganin surutun Inna Asabe ya lafa hakan ne yasa wata Tsaleliyar Budurwa ma'abociyar kyawun fasali gami da tsarin halitta ta fito daga cikin wani Ζaramin daki wanda daganin a'lamu da ada can ba Ιaki bane.
Cikin sanΙa da tafiya tamkar wata barauniya ta Ιauko, bokitin caples da wani katon tulu, Ιaukar tulun keda wuya sai ta sa gudu ta fito daga cikin gidan duk da tasan cewar ranar kashin ta ya bushe.
Tun lokacin da ta fito daga gidansu Bata tsa gaita da fyalla gudun nan ba har sai da ta tabbatar da cewar ta iso bayan gari.
Ni da nake binta a baya ban iya komai ba face kallo da muka shiga cikin ruΙani gami kauyanci domin komai iya gayun mutum, idan ya kalli yanayin gurin zai yi matukar mamaki domim kuwa tabbas wajen ya amsa sunansa abin kallo.
Cikin hanzari da Ιaga Ζafa ta iso izuwa bakin wata Ζorama wacce ko da ace ba'a damu Ιibar ruwan cikin ta to lallai ba Ζaramin so mutum zai yi ya ganshi ya kasance a tare da itaba wani sanyi take busawa marar cutarwa wanda idan zaka shekara a bakin wannan fadama kai da mura ko zafi sai wani ikon Allah.
Wani Ιan Ζaramin kwano ta Ιauko acikin bokitin caples Ιin ta samo kwaso ruwan a hankali domin bata shiga cikin sa saboda kiyaye lafiyar jikinta, cikin nutsuwa da kamala ta kammala cika bokin ta kaf baki Ιaya sannan ta koma kan tulun ruwanta shima ta cika.
Kammalawar hakan ke da wuya a gareta sai tayi hanzarin Ιaukar bokintin a ka sannan ta Ιauki tulun a hannun ta tanufi izuwa hanyar komawa gidansu domin bata san mai zai faru da ita ba ayau.
Tayi nisa cikin tafiyarta sai taga mutum tsulum a gabanta cikin firgici ta Ιago kai ta dube shi tana mai faΙin cewa subhanallahi.
Haba yaya Sa'idu don Allah yanzu wannan wasa ne? Gaskiya bana son irin wannan wallahi idan ka Ζaramin sai nai maka kuka.
Murmushi yayi sannan yace yi haΖuri Ζanwata na tuba, amma daga ina kike haka da yamma? Wallahi Inna Asabe ce ta ake ni tun da safe na Ιebo mata ruwa a rafin bayan garin don tace min tafi son ruwan can domin yafi tsafta da ΙaΙin sha, na Ιauko tulu zan tafi sai Iya tace sai na kammala ayyu kan gida ban kammala aikin ba ni kuma sai wajen La'asar don gudun fushin Inna Asabe shiyasa ka ga na tahon yanzu idan ba haka ba duka zatamin wallahi.
Hawaye ne ke zubowa daga fuskar Sa'idu yana mai cewa kiyi hakuri ZULAIHAT komai mai wucewa ne wata rana sai labari bani ruwan naki na kai miki gida ko don kiyi saurin zuwa kada taimaki faΙa hakan kuwa akai babu garda ta miΖa masa ya karΙa ya Ιora a kansa sannan ya riΖe tulun ruwan a hannu, suka soma tafiya a cikin tafiyar tasu Sa'idu ya fuskaci Zualaiha babu annuri ko kwanciyar hankali a tattare da ita hakan ne ya bashi Ζarfin gwiwar Ιauke mata tunanin ta da abubuwan dariya wani lokacin ma sai ya cakuleta da tsokana ita kuwa tai ta keta dariya kamar baza ta daina ba.
To Yan zu muka soma mai karatu sai ka Ιaura Ιamarar wanzuwa tare da niπ¨π½π»
Nakune:
Mrs: *Ali*
Sunday, July 15, 2018
LAMARIN DUNIYA Page 01
Tags
Aliyu Miko Muh'd#
Share This
About Hausa Fulani Writers
Aliyu Miko Muh'd
Labels:
Aliyu Miko Muh'd
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Post Top Ad
Your Ad Spot
No comments:
Post a Comment